Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an tsaro sun hallaka yan bangar siyasa uku a Kogi

Published

on

Yayin da ya rage Kwanaki 4 a shiga Zaben gwamnan jihar Kogi, hadakar jami’an tsaro sun halaka ‘yan bangar siyasa uku da ke tada zaune tsaye a Anyigba dake yankin mazabar dan majalisar tarayya ta tsakiya.

Mai magana da yawun rundunar SP William Ovye Aya, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya fitar yau Talata.

Sanarwar ta ce, jami’an tsaron sun sami wadanda ta kama da bindigogi guda biyu kirar AK47.

Haka kuma sanarwar ta ce, hadakar jami’an tsaron da suka hadar da na DSS da na Civil Defence, sun kai sumamen ne wani gidan da yan siyasa suka girke yan dabar siyasar domin cimma muradansu na kashin kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!