Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matasa fiye da 10 sun mutu a Kano sakamakon shan shayi da Zakami

Published

on

Al’ummar unguwar sheka da ke karamar hukumar Kumbotso na ci gaba zama cikin alhinin rashin matasan yankin da ake zargin sun kai goma sha biyu, sakamakon shan shayin zakami da suka yi yayin murnan wani bikin aure.

Malam Abdullahi Mahmud da Hajara Abdullahi  na daga cikin iyayen da suka rasu ‘ya’yansu sakamakon shan zakamin, a tattaunawarsu da Freedom Radio, sun bayyana cewa an shirya wa ‘ya’yan nasu makirci ne inda aka zuba musu Zakamin suka sha ba tare da sun sani ba.

Haka kuma sun bukaci mahukunta da su tabbatar da cewa an yi wa wadanda ke da hannu a lamarin hukuncin da ya dace.

A nasa bangaren kwamandan kungiyar sintiri ta Vigilante na yankin Malam Mahmud Isa Abubakar, ya tabbatar da cewa sun samu labarin afkuwar wannan mummunan lamari.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rundinar ‘yan sandan Kano, Ya ce, rundunar na kan gudanar da bincike a kan afukar wannan lamari, kuma za ta magantu nan ba da jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!