Labarai
Jami’an tsaron Chadi sun kama ɗan shugaban Boko Haram Mohammed Yusuf

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama dan shugaban ƙungiyar Boko Haram na farko a ƙasar Chadi mai suna Muslim Mohammed Yusuf.
An kama Musulim ne tare da wasu mutum biyar da ake zargin ƴan Boko Haram ne, ƙungiyar da mahaifinsa ya assasa a kasar nan a shekarun baya.
Rundunar ƴansandan Chadi ta tabbatar da kama ƴan Boko Haram shida, amma ba ta iya tantance ɗan Muhammad Yusuf a ciki ba, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.
Sai dai wata majiyar tsaro da kafar AFP ta zanta da su, sun tabbatar mata da kama ƴan Boko Haram shida, ciki har da shi Muslim ɗin.
An fi sanin Muslim da suna Abdrahman Mahamat Abdoulaye, kuma ƙani ne ga jagoran ISWAP Habib Yusuf, wanda aka fi sani da Abu Mus’ab Al-Barnawi.
You must be logged in to post a comment Login