Ƙetare
Jami’an tsaron tekun Tunisia sun tsamo gawarwakin yan ci-rani 29
Jami’an tsaron gabar tekun kasar Tunisia, sun sanar da tsamo gawarwakin wasu yan cirani su Ashirin da tara daga cikin ruwa wadanda suka fito daga kasashen saharar Afrika, biyo bayan kifewar jiragen kwale-kwale guda uku da ke dauke da su da nufin ratsa tekun don isa nahiyar Turai.
Wannan dai shi ne ibtila’i mafi muni na baya-bayan nan da aka gani a gabar tekun na Tunisia, makwanni kadan bayan kalaman shugaba Kais Saied da ke alakanta yan cirani bakar fata da suka fito daga kasashen saharar Afrika a matsayin masu aikata manyan laifuka a kasar.
Rahotonni sun bayyana cewa, daruruwan yan cirani ne ke rasa rayukansu a kan hanyarsu ta isa Turai daga gabar tekun da ke Tunisia wadda ke matsayin hanya mafi sauki ga masu son isa Turai amma kuma mai cike da hadari.
A lokuta da dama wasu ana rasa ganin ko da gawarsu bayan kifewar kwale-kwalen da ke daukarsu zuwa Turai.
You must be logged in to post a comment Login