Labarai
Jami’an ‘yan sada sun rufe kofofin shiga majalisun dokokin kasar
Jami’an ‘yansada sun rufe kofofin shiga majalisun dokokin kasar nan ta yadda suka hana shiga da fita na ma’aikatan dake a cikin zauren majalisun na kasa.
Jami’an tsaron sun kuma rufe babbar hanyar zuwa dandalin Eagle Square bayan da suka girki motocin sintiri don hana tashin tarzoma.
Sai dai jami’an tsaron sun bar manema labarai da ‘yan jaridu da ma’aikatan da suke aikin gine-gine da masu saida kayayyaki shiga cikin majalisar.
Tun a jiya ne dai ma’aikatan dake aiki a cikin majalisar karkashin Kungiyar gamayyar ma’aikata na majalisar suka tsunduma yajin aiki na gargadi na kwanaki 4 don biya musu bukatun su, yayin da suka sanya harkokin majalisar suka tsaya cak.