Labarai
Jami’ar Bayero ta kammala fassarar wasu litattafan kimiyya da lissafi zuwa harshen hausa
Jami’ar Bayero dake nan Kano ta Kammala fassarar fizis, PHYSICS Kyamistare CHEMISTRY, lissafi MATHEMATICS zuwa harshen HAUSA.
Cibiyar bincike kan Harsunan Nigeria da Fassara da hikimomin al’umma na jami’ar Bayero dake nan Kano da gudanar da aiki.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da babban daraktan cibiyar Farfesa Aliyu Mu’azu ya fitar a nan Kano cewa Litattafan sun hada da Kimiyya da Fasaha don makarantun Firamare, Littafi na daya zuwa na uku.
A cewar farfesa Aliyu Mu’azu cibiyar tayi Nasarar buga wa tare da fassara Litattafan kimiyya guda takwas zuwa harshen Hausa saboda daliban makarantun firamare dana Karamar Sakandare (Junior) da kuma babbar Sakandare (Senior) Saboda dalibai ‘yan yankin Arwacin Nigeria.
An bukaci a daga darajar kwalejin ilimi ta Nasiru Kabara zuwa jami’a
Dokar kafa hukumar bunkasa ilimi na jihar Kano ya tsallake karatu na 2
Majalisar dokoki za ta gyara dokar kafa hukumar samar da tallafin ilimi
Sai kuma Lissafi don Kananan makarantun Sakandare shi ma Littafi na daya zuwa na uku.
Kazalika sai kuma Kyamistare (Chemistry) don manyan makarantun Sakandare, da kuma Fizis (Physics) don manyan makarantun Sakandare.
Haka kuma wajen yin aikin wannan fassara Farfesa Mu’azu yace sunyi amfani ne da tsarin manhanja wato karantarwa na kasa (National Curriculum) tare da taimakon abokan aikin su na tsangayoyin kimiyya wato Faculty of Science da kuma na Faculty Of Education.
Farfesa Mu’azu yace “Shawarar fassara wadannan Litattafan da kuma buga su yazo ne sakamakon kokarin da wannan cibiya take yi na ganin ta bada nata gudun muwa wajen bunkasa ilimin zamani a yankin Arewacin kasar nan ta hanyar koyar da ilimin da harshen uwa (harshen Hausa).
A don haka wannan cibiya tayi amannar cewa koyo da koyarwa zai kasance mafi sauki da kuma fahimta matukar dai ana yi ne da harshen Hausa (Mothers tongue).
Farfesa Aliyu Mu’azu ya kara da cewa a kara da cewa kasashen da suka cigaba, sirrin cigaban ilimin su shine koyar da ilimi da suke yi da harasan su wato Harshen Uwa.
Babban darakatan Farfesa Mu’azu yace ” Cibiyar zatayi kokari wajen hada kai da hukumomin Jahohi dana tarayya dan tabbatar da cewa wadannan Litattafan ana amfani dasu a makarantun kasar”
A jawabin sa mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Muhammmad Yahuza Bello yace “Yayi alkawarin taimakawa duk wani cigaba da wannan cibiya ta kawo don bunkasa Hausa da kuma amfani da harshen Uwa (Mothers tongue) a arewacin Nigeria dama kasa baki daya