Labaran Kano
Jami’ar Bayero ta yi bikin yaye dalibai karo na 35
Jami’ar Bayero ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa ga dalibai.
Shugaban jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye dalibai karo na 35 da aka gudanar a dakin taron yaye dailbai dake harabar jami’ar a yau Litinin.
Ya ce daya daga cikin matakan da suka dauka wajen cimma wannan buri sun hadar da baiwa masu bukata ta musamman damar yin zarra a kwasa-kwasai daban-daban da kuma tallafawa dalibai masu karamin karfi guraben karatu da jami’ar zata rinka yi a kowace shekara.
A yayin bikin na yau dai tsangayun nazarin aikin noma da Kwamfuta da fasahar sadarwa da kuma na ilmi ne suka yaye daliban nasu da suka samu daraja daban-dabam, inda kuma tuni jami’ar ta fara sabbin kwasa-kwasai a bangaren Injiniya da manhajar Kwamfuta da kuma tsaron yanar sadarwa.