Kiwon Lafiya
Jami’ar Jigawa ta Sule Lamido ta lashe gasar mahawara jam’io’in Afrika ta Kudu
Jami’ar jihar jigawa ta Sule Lamido ta sami nasarar lashe gasar mahawara ta Jami’o’in kasashen Afrika ta Yamma karo na 2 ta bana.
Jami’ar ta Sule Lamido dake Kafin Hausa ta sami nasarar ne a yayin gasar da aka yi a kasar Ghana da aka yi a tsakanin ranar 7 zuwa 11 ga wnnan watan da ya hada da kasashen Ghana da jamahuriyyar Benin da kuma nan Najeriya.
Ana dai gabatar da gasar kamar yadda ake yi majalisar dokokin Burtaniya, yayin da za’a sanya mutum hudu su zama masu tafiyar da gwamnati yayin da ‘yan adawa kuma za su tafka mahawara kan kudirin da gwamnatin ta gabatar, kafina yankin hukunci dafa karshe bayan kudirin ya tsallake karatu 5 an kuma tafka mahawara.
Jagoran Tawagar daliban jami’ar ta Sule Lamido da suka wakilci Najeriya a yayin gasar sun hada malaman Idris Hamza Yana da kuma daliban sun hada da Aisha Goni da Alhassan Tsalhatu da Haruna Abdurrahaman da Ibrahim Hussaini Yakubu Da yake tarbar daliban bayan sun dawo daga gasar Shugaban jami’ar farfesa Lawan Sani Taura ya taya su murna saboda jajircewar da suka yi, yana mai cewar kasancewar su jakadu na gari hakan zai dauka jami’ar kai wa mataki na gaba