Labaran Kano
Jami’ar NOUN za ta fara koyar da harsunan Hausa, Larabci da Yarbanci
Jami’ar karatu daga gida ta NOUN za ta fara koyar da Kwasa-Kwasan harsunan Hausa da Larabci da Yarbanci da Igbo cikin tsarin koyo da koyarawar ta domin baiwa dalibai damar samun ingantaccen ilimi.
Shugaban Jami’ar ta NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan Freedom Rediyo.
Farfesa Abdallah Uba ya kara da cewa, jami’ar ta amince da kwasa-kwasan ne saboda yawanci wanda ke karatu a jami’ar yan kudu ne, inda ya ce fara koyar da wannan kwasa-kwasai zai baiwa yan arewacin kasar nan dama shiga jami’ar.
Shugaban ya koka kan yadda wasu daga cikin al’umma musamman ma ‘yan arewa ba su yarda da tsarin wannan jami’ar ba duk da irin kokarin da suke na wayar da kan al’umma wanda hakan ya sanya ‘yan kudancin kasar nan suka mamaye jami’ar.
Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kuma bayyana cewar ingancin karatu a jami’ar dai-dai yake da sauran karatun jami’o’in dake kasar nan.
Labarai masu alaka:
Jami’ar NOUN ta gargadi dalibai masu takarardun bogi
Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.