Connect with us

Labarai

Fadar shugaban kasa ta gargadi kasashen Turai

Published

on

Fadar shugaban kasa ta gargadi kasashen Amurka da Burtaniya da kuma tarayyar turai da su guji tsoma baki cikin lamuran da ya shafi kasar nan,musamman zargin take hakkin bil adama.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka ta cikin shirin gidan talabijin na Channels mai taken: Politics Today’ kan zargin da kasasen ke yi ga kasar nan na take hakkin bil
adama.

Mr Femi Adesina ya ce Najeriya kasa ce mai ‘yanci saboda haka ko da wasa ba za ta bari wata kasa ta rika tsoma    mata baki cikin harkokinta na cikin gida ba.

Da aka tambaye shi kome zai ce game da samamen da jamian hukumar tsaro ta DSS su ka kai kotu da kuma kama mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore, Femi Adesina ya ce, Najeriya ba kasa ce da ta ke amsar umarni daga kasar Amurka ko Burtaniya ko kuma tarayyar turai ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!