Siyasa
Jam’iyyar APC ta kammala zaben shugabanninta na kananan hukumomin Kano da aka fara a karshen makon da ya gabata
A yau ne jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kammala zaben shugabanninta na kananan hukumomi da aka fara a karshen makon da ya gabata jihohin Najeriya 36 inda jihar Kano ta kammala nata zaben Asabar din nan a shalkwatar Jam’iyyar da ke unguwar Hotoro a yankin karamar hukumar Tarauni, da kuma sauran kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Hausa.solacebase ta samu kai ziyara kananan hukumomin Tarauni da Kano Municipal da Gwale da kuma karamar Hukumar Dala, inda a wadannan kananan hukumomi zaben ya gudana cikin lumana.
Wasu daga cikin wadanda suka kada kur’ar su yayin zaben sun shaida wa Solacebase cewa zaben yana gudana ne cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Abdullahi Dan Sumaila, shi ne jami’in da ke kula da zaben a Karamar Hukumar Gwale ya shaida wa Wakilinmu cewa sun dauki mataki kan yadda za’a kammala zaben cikin lumana a karamar hukumar ta Gwale.
Da yake zantawa da manema labarai, Kwamishinan yada labarai Matasa, wasanni da al’adu na Jihar Kano kwamared Muhammad Garba ya ce alamun zaben na nuni da yadda jihar Kano ta yi fice wajen da’a da kaunar zaman lafiya da cigaban Dimukuradiyya.
Kwamishinan yada labaran ya kuma Shawarci sauran ‘ya‘yan jamma’iyar ta APC da su ci-gaba da bayar da hadin kai don ci-gaban Dimukuradiyya da na Kasa baki daya.