Labarai
Jam’iyyar PDP na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taron ta na kasa

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taron ta na ƙasa a Ibadan duk da sabon hukuncin kotuna da rikice-rikicen cikin gida.
An tsara taron ne domin gudana shi a ranar 15 da 16 ga watan da muke ciki na Nuwamba.
A makon da ya gabata, Kotun Jihar Oyo ta bawa jam’iyyar damar cigaba da shirin taron.
Sai dai daga baya wata kotu a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da shi tare da hana INEC halarta ko amincewa da duk wani abu da ya shafi taron, wanda hakan ya jefa jam’iyyar cikin rudani.
Wani sashe na jam’iyyar da Sam Anyanwu ke jagoranta ya sanar da dage taron, amma shugabancin jam’iyyar na Umar Damagum ya musanta hakan, yana mai cewa babu wani hukuncin kotu da ya isa ya dakatar da shirye-shiryen.
You must be logged in to post a comment Login