Labarai
Jam’iyyar PRP ce za ta tsamo Najeriya daga halin da take ciki – Dakta Durojaiye
Mai neman takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓen 2023, ƙarƙashin Jam’iyar PRP Dakta Abdulfatah Durojaiye, ya ce Najeriya za ta dawo hayyacinta da zarar al’umma sun zaɓi jam’iyyar PRP.
Dakta Durojaiye ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano, lokacin da yake zantawa da manema labarai, tare da bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar PRP.
A cewar sa lokaci yayi da al’ummar Najeriya za su dawo daga rakiyar manyan jam’iyyu su dubi managartan al’umma a cikin ƙananan jam’iyyu masu tasowa da za su bunƙasa ƙasa tare da samar mata da ci gaban da ake ta ikirarin sa tsawon shekaru Sittin.
“Na yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a matsayina na mai kishin ƙasa kuma ɗan ƙasa da nake son bada tawa gudummawar musamman ma wajen inganta Ilimi da harkokin lafiya”.
“Za mu samar da Ilimi kyauta tun daga matakin Firamare zuwa makarantun gaba da Sakandire tare da bunƙasa harkokin kiwon lafiya da samar da cikakken tsaro da bunƙasa karkara don samar da ayyukan yi ga ɗumbin matasa” inji Dakta Abdulfatah Durojaiye.
Ɗan takarar ya ce kawo yanzu haka jam’iyyar ta PRP ita kaɗai take da tsararrun manufofi na bunƙasa ƙasa da al’umma, ba kamar sauran Manyan jam’iyyun ƙasar ba da kawai suna kafa gwamnatoci ne a matakin ƙasa da jihohi ba tare da tsayayyiyar manufa ba.
You must be logged in to post a comment Login