Labarai
Janar Christopher Musa ya musanta yin murabus daga muƙaminsa

Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin yin murabus daga muƙaminsa.
Hakan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa ministan kan Kafafen Yaɗa Labarai, Leah Katung-Babatunde, ya fitar a baya baya nan.
Sanarwar ta ce, labarin da ake yaɗawa cewa ministan na shirin murabus labari ne na ƙanzon kurege da ba shi da tushe balle makama.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Christopher Musa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na tsaron ƙasa.
Haka kuma, sanarwar ta buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai daga ofishinsu kafin yaɗa su.
You must be logged in to post a comment Login