Labarai
Kashim Shettima ya yi Allah-wadai da hare-haren kyamar baki a Afirka ta Kudu

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi Allah-wadai da hare-haren kyamar baki da aka kai wa ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka a kasar Afirka ta Kudu, da ya buƙaci ƙasashen ECOWAS su kai batun gaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka AU domin a nuna cewa ba za a amince da irin wannan ɗabi’a ba.
Kashim Shettima, ya bayyana hakan ne a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin taron shugabannin ƙasashen ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a Lungi na ƙasar Saliyo.
A cewar sa Najeriya na kallon hare-haren a matsayin ƙin jinin ’yan Afirka kuma ya kamata ƙasashen yankin su haɗa kai wajen magance matsalar.
Ya kuma tunatar da Afirka ta Kudu irin gudunmawar da ƙasashen Afirka, musamman Najeriya, suka bayar wajen yaƙin neman ’yancin ƙasar daga mulkin wariyar launin fata.
You must be logged in to post a comment Login