Labarai
Jigawa: Yan sanda sun fara bincike kan rasuwar dattijo a dakin Otal

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta fara bincike kan mutuwar ba-zata da aka samu a wani otal da ke cikin birnin Dutse, yana yin da zama akwai zargi.
A ranar Talatar nan 21 ga Yuli wannan shekara ta 2026 namacin, mai shekaru 60, ya shiga otal ɗin tare da wata budurwa mai shekaru 20, kuma bayan ya nemi a kawo masa abinci sai ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi.
Da samun rahoton ne Rundunar ta tura jami’an ta na Sashen Yalwawa cikin gaggawa tare da garzayawa da mutumin zuwa babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa bayan yan gwaje-gwaje.
Tini dai Jami’an dake bincike suka killace wurin da abin ya faru tare da gudanar da bincike kan abinci da abubuwan sha, ciki harda wani sinadari da ake zargin na ƙara ƙarfin jima’i ne, da wasu kayayyakin marigayin domin ci gaba da bincike.
A cewar Rundunar bayan an kammala duk matakan da suka dace, an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana’iza bisa ga buƙatarsu, ya yin da Budurwar da ke tare da shi a lokacin da ya faru ke ci gaba da baiwa jami’an dake bincike haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen aikin da suke.
You must be logged in to post a comment Login