Jigawa
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke matashin da ake zargi da kashe mahaifinsa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, ta kama wani matashi mai shekaru 26 da take zarginsa da hallaka mahaifinsa ta hanyar sassarashi da makami.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Lawan Shisu Adam, ne ya shaida wa Freedom Radio hakan.
Ya ce, lamarin ya afku ne a garin Sara da ke yankin karamar hukumar Gwaram ta jihar.
Haka kuma, ya ƙara da cewa za su gurfana da matashin da zarar sun kammala bincike.
You must be logged in to post a comment Login