Labarai
Jigawa: Jami’an Civil Defence sun kama mutane 20 bisa zargin sare bishiyoyi

Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Jigawa, ta kama wasu mutane 20 da ta ke zargi da laifin sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba domin yin Gawayi.
Kwamandan hukumar a jihar Jigawa Alhaji Muhammad Kabiru Ingawa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, a wani bangare na yunkurin hukumar na dakile aiyukan da suka saba ka’ida da dokoki.
A cewar Ingawa sun fara daukar wannan mataki ne biyo bayan samun rahoton yawaitar sare saren bishiyoyi barkatai da wasu ke aikatawa a jihar, bisa manufar yin Gawayi da samar da itacen wuta wasu kuma Katako.
Ya ce sun kama mutane 10 bisa zargin sare bishiyoyi don yin Gawayi da katako a yankin karamar hukumar Birninkudu sai wasu guda 6 a yankin karamar hukumar Kazaure da kuma karin wasu guda 4 bisa sare bishiyoyi suna yin katako.
Haka kuma, ya kara da cewa dukkan wadan da ake zargin an mikasu ga hukumar Kare muhalli ta jihar Jigawa kafin daga bisani a gurfanar dasu a gaban kuliya.
You must be logged in to post a comment Login