Connect with us

Labarai

Jonathan ya musanta karbar kudi don raba ƙuri’un yankinsa

Published

on

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta rahoton da ke zargin cewa an yi masa tayin Naira biliyan 500 ko kuma ya na da hannu a wani shiri na raba ƙuri’un yankin Kudu Maso Kudu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

 

Jonathan ya bayyana rahoton a matsayin na ƙarya marar tushe, tare da yin kira ga ’yan Nijeriya da su yi watsi da shi.

 

A cikin wata sanarwa da Mai ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dakta Ikechukwu Eze, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce rahoton ƙagaggen labari ne da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a da kuma jefa tsohon shugaban ƙasar cikin cece-kuce na siyasa.

 

Ya jaddada cewa Jonathan bai taɓa halartar wani taro ko shiga wata tattaunawa ko yarjejeniya da ta shafi wannan zargi ba.

 

Eze ya bayyana cewa tun bayan barin mulki a shekarar 2015, Jonathan ya ci gaba da kasancewa jagoran ƙasa mai mutunta dimokuraɗiyya, inda yake inganta zaman lafiya, shugabanci nagari da ingantaccen tsarin dimokuraɗiyyar a Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika. 

 

Mai taimaka masa kan yaɗa labarai ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da al’umma su riƙa tantance sahihancin rahotannin siyasa masu muhimmanci kafin wallafawa ko yaɗa su. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!