Connect with us

Labarai

Majalisar dokoki ta bukaci a kai wa mutanen Sumaila dauki kan ambaliyar Ruwa

Published

on

Majalissar dokokin jihar Kano, ta karɓi ƙudurin gaggawa na buƙatar gwamnatin jihar da hukumar bada agajin gaggawa SEMA da su kai ɗauki garin Sumaila da Magami a ƙaramar hukumar Sumaila, bisa iftala’in ambaliya da ta sabbaba rushewar gidaje a garuruwan biyu.

 

A zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Jibril Ismail Falgore, wakilin Sumaila, Zubairu Hamza Massu, ne ya gabatar da ƙudurin.

 

Zubairu Massu ya ce, a halin da ake ciki yanzu mutanen yankin na cikin tashin hankali da suke buƙatar taimakon gaggawa.

 

A makon da ya gabata majalisar ta kafa kwamiti da zai riƙa lura tare da duba irin wannan iftala’in don magance shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!