Labarai
Jigawa: Ma’aikatu da Hukumomi sun fara kare kasafinsu na badi a Majalisar dokoki

Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin jihar Jigawa sun fara ziyartar kwamitocin Majalisar dokoki domin kare kasafin kudinsu na badi bayan Gwamna Malam Umar Namadi ya gabatarwa da zauren majalisar kunshin kasafin kudin a satin Daya gabata.
Kwamitin Kudi na Majalisar Karkashin Jagorancin Lawan Muhammad Dansure shine ya bude fara kare Kasafin kudin inda Hukumomin dake Karkashin Ma’aikatar Kudi kamar Hukumar tattara Kudaden shiga ta jiha da Ofishin babban Akanta suka bi Sahu.
Haka kuma kwamitin dake Kula da ayyuka na musamman da kwamitin Kula da bada agajin gaggawa sun gurfana a gaban kwamitocin dake karkashinsu.
Wakilin Freedom Radio a majalisar dokokin ta Jigawa, ya ruwaito cewa, yayin tantance Kasafin kudin kwamitocin Majalisar zasu bukaci bayanai daga bangaren Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin kan yadda zasu kashe Kudaden da aka ware musu a kunshin kasafin kudin.
You must be logged in to post a comment Login