Jigawa
Jigawa: Mutane 2 sun rasu 7 sun jikkata sakamakon rikicin Manoma da Makiyaya

A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garin Dagaceri a karamar hukumar Birniwa, ta jihar Jigawa.
Rahotonni sun bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne bayan wani sabani da aka samu tsakanin wani makiyayi da manomi, wanda daga bisani ya rikide ya zama rikici mai tsanani tsakanin al’ummomin yankin.
Jami’an tsaro sun isa wajen da lamarin ya faru domin dawo da doka da oda, yayin da aka tabbatar da cewa an kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ba su kulawar jami’an lafiya.
You must be logged in to post a comment Login