Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Jihar Abia tayi Allah wadai da harin da aka kai wa yan wasan Enyimba a Jos

Published

on

Gwamnatin jihar Abia ta yi Allah wadai da farmakin da aka yiwa ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Enyimba a garin Jos dake jihar Plateau.

Lamarin dai ya afku ne bayan rashin nasara da suka yi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Plateau United a ranar Lahadi 27 ga watan Yunin 2021, a gasar cin kofin kwararru ta Najeriya.

‘Yan wasan Enyimba biyu, mai tsaron baya Dare Olatunji da mai tsaron raga Sabirou Bassa-Djeri ne suka samu rauni yayin rikicin.

Rikicin ya biyo bayan jan kati da aka baiwa dan wasa Timothy Danladi sakamakon rashin kyautawa, lamarin ya sanya dan wasa yin fushi tare da ficewa daga filin hakan ya fusata magoya bayan Plateau United har ya kaiga rikici.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!