Manyan Labarai
Jihar Jigawa ta yi wa Kano fintinkau a taimakawa marasa karfi
Gwamnatin Jahar Jigawa tayi wa Kano nisa wajen inganta rayuwar marasa karfi a jihar.
Wannan na tattare ne cikin wasu bayanai bayan kammala shirin tattaunawa da ‘’yan majalisun jihar Kano da na Jigawa akan tsarin samar da dokar nan ta taimakawa marasa karfi da ya gudana a birnin tarayya da ke Abuja.
Shi dai tsarin na social protection wanda kungiyar Action against hunger da hadin kan kungiyar save the children ta fito da shi ,ya bayar da damar kariya ga yara wadanda suke cikin rashin koshin lafiya.
Daya daga cikin mahalatta taroin kuma dan majalisar dattijai daga jihar Jigawa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia yace kasashe da dama a Duniya da ake ganin sun cigaba ,sun samu hakan ne ta hanyar bawa marasa karfi wasu damammaki da ya hada da bayar da jari.
Ibrahim Hassan Hadejia yace da ace kasashe irin su Birtaniya da Amurka da sauran kasashen Duniya za su daina bayar da taimako ta hanyar social protection da tuni wadannan kasashen talauci yayi mu su katutu.
Daga nan an bukaci ‘’yan majalisun jihohin na Kano da Jigawa da su fito da dokoki na taimakawa mara sa karfi.
Ita dai jahar Jigawa a yanzu tana ware kimanin fiye da Naira biliyan daya duk shekara a matsayin kudade na taimakawa marasa karfi da kuma tsarin kosar da yara.