Connect with us

Labarai

Jihohi Bakwai za su fuskanci rashin wutar lantarki – NISO

Published

on

Kamfanin Kula da Wuyar Lantarki mai zaman kansa na kasa NISO ya sanar da cewa jihohi bakwai za su fuskanci ƙarancin wutar lantarki na tsawon makonni shida sakamakon wani shirin gyara da aka tsara a layin wutar Jos zuwa Gombe.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar,  ya ce za a fara aikin daga ranar 9 ga Afrilun da muke ciki zuwa 22 ga Mayu mai kamawa.

NISO ya bayyana cewa za a riƙa samun katsewar wutar ne duk mako daga ranar Alhamis zuwa Lahadi, tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, domin kafa wayar sadarwa ta “fibre optic”.

Jihohin da abin zai shafa sun hada da Plateau, Gombe, Bauchi, Borno, Adamawa, Taraba da Yobe.

Kamfanin ya ce wannan gyara na daga cikin ƙoƙarin sabunta tsarin lantarki na ƙasa domin inganta aiki ta hanyar amfani da sabbin fasahohi, tsarin sarrafa makamashi, da kuma ingantaccen sadarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!