Labarai
Jihohin ƙasar nan 36 sun kai gwamnatin tarayya ƙara gaban kotu
Jihohin ƙasar nan 36 sun shigar da ƙara gaban kotun ƙoli bisa zargin gwamnatin tarayya da ƙin shigar da kudaden da aka ƙwato zuwa ga asusun tarayya.
Ta hannun Lauyoyin su, masu shigar da ƙarar sun ƙaddamar da matakin kan ministan shari’a kuma Attorney janar Abubakar Malami.
Masu shigar da ƙarar suna neman a bayyana musu yadda aka yi da kuɗaɗen kamar yadda sashi na 162 (1) da sashe na 162 (10) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan na shekarar 1999 ya tsara cewa, dukkanin kuɗaɗen da aka ƙwato wajibi ne a sanya su a asusun tarayya a kuma fitar da rasiti.
Sun kuma roƙi kotun da ta bayyana cewa abinda ministan shariar yayi ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana wanda shi ne ya jagoranci shigar da ƙarar a watan Yuni a madadin jihohi 36 ya ce har yanzu kotun ƙolin ba ta bayar da ranar da za a ci gaba da sauraran ƙarar ba.
You must be logged in to post a comment Login