Connect with us

Addini

Jiragen yaƙin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta kan Zirin Gaza da safiyar laraba

Published

on

Rahotanni daga gabas ta tsakiya na cewa jiragen yaƙin sojin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a Zirin Gaza da ke yankin Palastinu a wayewar garin yau laraba.

 

Rahotanni sun ce tun a cikin daren jiya sojojin Isra’ila suke ta kai hare-hare ta sama a birnin lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane  masu yawa.

 

Wasu mazauna birnin sun bayyana cewa, hare-haren ya shafi muhimman wurare na birnin ciki har da ofisoshin gwamnati.

 

Gidan talabijin na Aljazeera ya ruwaito cewa, a unguwar Tel al-Hawa, wani magidanci da matar sa mai dauke da juna biyu da kuma ɗansu ɗan shekara biyar sun rasa rayukansu sakamakon hari ta sama da jiragen yaki na Isra’ila suka kai a gidansu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!