Addini
Jiragen yaƙin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta kan Zirin Gaza da safiyar laraba

Rahotanni daga gabas ta tsakiya na cewa jiragen yaƙin sojin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a Zirin Gaza da ke yankin Palastinu a wayewar garin yau laraba.
Rahotanni sun ce tun a cikin daren jiya sojojin Isra’ila suke ta kai hare-hare ta sama a birnin lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa.
Wasu mazauna birnin sun bayyana cewa, hare-haren ya shafi muhimman wurare na birnin ciki har da ofisoshin gwamnati.
Gidan talabijin na Aljazeera ya ruwaito cewa, a unguwar Tel al-Hawa, wani magidanci da matar sa mai dauke da juna biyu da kuma ɗansu ɗan shekara biyar sun rasa rayukansu sakamakon hari ta sama da jiragen yaki na Isra’ila suka kai a gidansu.
You must be logged in to post a comment Login