Labarai
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ya lalace zai koma aiki nan da kwana 10- Minista

Ministan sufurin Najeriya, Sa’idu Ahmed Alkali, ya ce nan da kwana goma layin dogo da kuma jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ya lalace zai koma aiki.
A wata ziyara da ministan sufurin ya kai wajen da jirgin ya kauce hanya jiya Litinin, ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da tsaron fasinjojin da sauran ma’aikatan jirgin har aka kwashe su.
A makon jiya ne dai jirgin ƙasan ya kauce hanya, inda ya tuntsure a kusa da tashar Asham bayan ya taso daga Abuja zai tafi Kaduna ɗauke da mutum 618, ciki har da fasinja 583 da ma’aikatan jirgin ƙasan guda 15 da ma’aikacin jinya 1 da masu goge-goge 11, sannan aƙalla fasinjoji bakwai ne suka ji rauni.
A lokacin da jirgin ya tuntsure, jirgin yana tafiya ne da tarago guda bakwai.
You must be logged in to post a comment Login