Labarai
Jirgin Sojin saman Najeriya ya kama da wuta bayan ya yi mummunan hadari

wani jirgin yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda matuka biyu suka tsira daga cikin jirgin kafin ya kama da wuta, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa jirgin ya tashi ne daga sansanin sojin sama na Kainji, kuma al’ummar yankin sun ce abin ya faru ne misalin ƙarfe 4:10 na yammacin jiya Asabar, inda aka ga wutar da ta tashi daga wurin da jirgin ya fāɗi.
You must be logged in to post a comment Login