Labarai
Jirginmu mai lamba C-130 da ke hanyar zuwa Portugal ya yi saukar gagga- Rundunar Soji

Rundunar sojin saman kasar ta bayyana cewa wani jirgin ta mai lamba C-130 da ke kan hanyar zuwa Portugal ya yi saukar gaggawa ta matakin kariya a birnin Bobo-Dioulasso, na Burkina Faso, bayan ma’aikatan jirgin sun lura da wata matsalar fasaha jim kaɗan bayan tashin sa daga Lagos a ranar 8 ga Disamba 2025.
Mai magana da yawun rundunar Air Commodore, Ehimen Ejodame ne ya bayyana hakan da ya ce an bi duk ka’idojin tsaro na ƙasa da ƙasa, kuma dukkan ma’aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya tare da kyakkyawar karɓa daga hukumomin ƙasar.
Rundunar Sojin saman ta ce shirye-shiryen ci gaba da aikin da aka tsara suna tafiya, ba tare da samun tangarda ba ko kuma matsalar diflomasioyya.
You must be logged in to post a comment Login