Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ka gaggauta biyan hakkin ‘yan fansho da ya kai Naira biliyan 26 – NLC ga Ganduje

Published

on

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta biyan bashin kudin ‘yan fansho da garatuti da kuma hakkin ma’aikatan da suka rasa rayukansu wanda ya kai jimillar sama da naira biliyan 26.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya bayyana haka yayin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara da kungiyar NLC da takwararta ta TUC suka shirya yau anan Kano.

Da ya ke jawabi yayin taron, Kwamared Kabiru Ado Munjibir, shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano, ya kuma bukaci gwamnatin da ta duba batun kara wa’adin shekarun aiki ga ma’aikatan jiha dana kananan hukumomi kamar yadda aka yiwa malamai.

Inda ya yi kira ga gwamnati da ta biya bashin ariya na ma’aikatan kananan hukumomi da aka karawa girma a wajen aiki har sau uku zuwa hudu, amma ba a taba biyansu hakkinsu ba.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasar reshen jihar Kano a bangare guda, ya shawarci gwamnati da ta fadada komar tattalin arzikinta, ta hanyar bullo da sabbin dabarun samun kudaden shiga na cikin gida

A nasa jawabin tsohon sakatare janar na kungiyar kwadago ta kasa kwamared Salisu Nuhu, ya kalubalanci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su yi bayani kan dalilan da ya sanya ake batun rashin isassun kudi a asusun tarayya.

Shugabannin kungiyar kwadago ta kasar dai sun kuma yabawa ma’aikatan jihar Kano sakamakon hazaka da kuma juriya da suke nunawa a wajen aiki, inda suka sha alwashin cewa ba za su taba bari gwamnati ta warware alkawuran da ta dauka na ci gaba da biyan mafi karancin albashi na naira dubu talatin da dari shida ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!