Manyan Labarai
Kabilar Igbo ba zasu iya shugabantar Najeriya su kadai ba- Rochas Okorocha.
Tsohon Gwamnan jahar Imo kuma dan majalisar dattijai Sanata Rochas Owelle Anayo Okorocha, ya bayyana cewa kabilar Igbo ba zai yiwu su sami shugabancin Najeriya su kadai ba, har sai sun hada kai da sauran kabilun Najeriya.
Sanata Rochas Okorocha ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a nan Kano bayan halattar wani daurin aure da yayi a fadar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.
Rochas Okorocha yace babu wani abu da zaka kira da suna shugabancin kabilar Igbo sai dai shugaban Najeriya da ya fito daga kabilar Igbo.
Sanata Okorocha yace kudu maso gabashin Najeriya a cikin tsarin tarayyara Najeriya yake, saboda haka babu wani dan asalin kabilar Igbo da zai zama shugaban Najeriya har sai ya samu goyon bayan sassan kasar nan.
Ya kara da cewa hakan yana da amfani kwarai da gaske wajen ganin Najeriya ta dinke a matsayin kasa daya.
Sannan tsohon gwamnan na jahar Imo yace ya zo Kano ne domin ya ga abokinsa kuma gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje .
Rochas Okorocha ya koka da rikicin da yake faruwa a jam’iyyar APC tsakanin shugaban ta na kasa Adams oshiomole tare da gwamnan jahar Edo Godwin Obaseki wanda yace hakan na iya jawo wa jam’iyyar matsalar faduwa zabe a zaben shekarar 2023.