Connect with us

Labarai

Mata a karamar hukumar Warawa sun karbi tagomashi

Published

on

Sama da mata dari biyu Gwamnatin tarayya ta baiwa jarin Naira dubu goma goma a karamar hukumar Warawa domin su dogara da kansu.

Guda na Hukumar Samar da ayyukanyi ta kasa National Directorate of Employment  NDE Alhaji  Sanusi Yakasai ne ya bayyana hakan yau lokacin bikin rabon jari ga mata ‘yan Asalin karamar hukumar Warawa  dari biyu.

A cewar sa tun daga lokacin da Shugaban kasa Buhari ya hau kan mulki yayi alkawarin cigaba da yaki da Talauci domin bunkasa tattalin arzikin al’ummar kasar nan.

 

Alhaji Sanusi Musa ya kuma yi kira ga matan da suka ci gajiyar samun rabon jarin da su rike jarin hannu biyu- biyu tare da cigaba da gudanar da sana’oin su cikin taka tsan-tsan domin bunkasa jarin na su.

Tasirin talla ga ‘ya’ya Mata

Kungiyar Save the children da Action against hunger sun kaddamar da Shirin tallafawa al’umma a jihohin Kano da Kaduna.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa cikin wadanda da suka  halarci taron akwai Dagacin Garin Dau Alhaji Musa Adamu Musa da Babban Limamin  garin Dau da sauran al’ummar Karamar hukumar ta Warawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,813 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!