Labarai
Kabilu a jihar Plateau sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
Hausawa da Fulani da sauran mazauna yankunan karamar hukumar Bokkos a jihar Plateau sun sanya hannu a takardar yarjejeniyar zaman lafiya a yankunan na su.
Al’ummar sun sanya hannu a yarjejeniyar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na kwana guda da kungiyar kiristoci ta Pentecostal ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID).
Manajan shirye-shirye na hukumar USAID Dakta Philip Hayab ya ce an shirya taron ne da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’ummar yankin.
“Sanya hannu kan yarjejeniyar wani bangare ne dake nuna jajircewa don inganta zaman lafiyar al’umma,” in ji Hayab.
You must be logged in to post a comment Login