Labarai
Kada a yi dabi’ar nan ta a mutu-ko-a-yi rai a zaben jihar Edo – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da suka tsaya zabe a jihar Edo da su guji dabi’ar nan ta ko-a-mutu ko-a-yi rai a yayin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a gobe Asabar.
Shugaban kasa Buhari ya aikewa masu kada kuri’a da yan siyasa da jami’an tsaro da su kiyaye abinda zai haifar da rikici a zaben.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar na cewa shugaba buhari na fatan ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hanakali da lumana tare da bin doka.
Sanarwar ta ce Buhari ya jaddada kudirinsa na ganin ana gudanar da mulkin dimukradiyya cikin tsari a kasar nan wanda hakan ba zai samu ba har sai ‘yan siyasa sun bada gudunmawa.
You must be logged in to post a comment Login