Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Kaduna za ta karbi tsarin tsaro na AMOTEKUN

Published

on

Kungiyar kudancin jihar Kaduna (SOKAPU) sun ce suna nazari dangane da karbar tsarin tsaro da ‘yan Kudu maso Yamma suka yi yunkurin samar da tsaro mai lakabi da AMOTEKUN a yunkurin kare kansu daga rikice-rikicen da tabbatar da zaman lafiya a yankin su.

 

Kungiyar ta ce suna nazarin karbar tsarin tsaron na AMOTEKUN, biyo bayan yawan hare-haren da ake kai wa mazauna yankin nasu na Kudancin Kaduna a shekarun da suka wuce.

 

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar Shugaban kungiyar, Jonathan Asake, ya ce kimanin mutane 35 ne suka rasa rayukan su a yankuna 10 na kudancin jihar, inda aka yi garkuwa da kimanin mutane 115 tun daga watan Junairun shekara ta 2020.

 

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da suka tsira, ya tursasa musu zama a sansanin yan gudun hijira da ake da su inda aka yi garkuwa da kimanin mutane  58 daga cikin su.

 

Asake ya bayyana tsarin na AMOTEKUN da yankin kudancin jihar Kaduna da za ta dauka a matsayin hanyar da ta dace wajen kare matsalolin rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi,tare da cewar ‘yan yankin nasu na goyon bayan wannan sabon tsarin da gwamnonin Kudu maso Yammancin kasar nan suka bullo dashi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!