Labarai
Kafin bude makarantu gwamnati ta kare dalibai daga corona -Majalisar dinkin duniya
Majalisar dinkin duniya ta shawarci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa ta dauki matakan da suka kamata don kare dalibai daga kamuwa da cutar corona, kafin bude makarantun kasar nan.
Majalisar ta kuma ce a kalla daliban firamare da na sakandire sama da miliyan arba’in da shida ne a Najeriya ke cikin hatsarin kamuwa da cutar corona, idan ba a dauki matakan kariya ba, bayan bude makarantun.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mista Edward Kallon.
Mista Edward Kallon, ya kuma ce, bai wa dalibai kariya shi ne abu mafi mahimmanci da ya kamata gwamnatoci su mayar da hankali don tabbatar da an kare lafiyar su a yayin neman ilimi.
You must be logged in to post a comment Login