Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

PACC ta tsare ‘dan Ali Baba da mukarrabansa hudu

Published

on

8:30pm

Har zuwa wannan lokaci hukumar Anti Corruption na ci gaba da tsare, dan gidan mai baiwa gwamnan Kano shawara kan al’amuran addini da kuma sauran  mukarrabansa hudu, kuma har zuwa yanzu hukumar ba ta ce komai ba kan binciken da ta ke, da kuma lokacin da zata gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

5:20pm

Sai dai da misalin karfe 5 da mintuna 13, hukumar Anti Corruption ta bayar da belin Ali baba Agama lafiya, amma kuma an ci gaba da rike dan sa Huzaifa tare da mukarrabansa hudu, inda suke ci gaba da amsa tambayoyi.
Sauran wadanda aka tuhuma tare da Huzaifan sun hada da Nasiru Chuwa, da Auwal Okal da kuma Garba Isa, sai kuma Zulkifilu wanda ake zargin ya arce.

Kai tsaye: Ali Baba da dansa sun gurfana a gaban Anti Corruption

Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran addina Ali Baba Agama Lafiya da dansa Huzaifa Ali Baba suna tsaka da amsa tambayoyi a gaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Kano.

Tun da farko shugaban hukumar Anti Corruption Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, sun samu korafi kan zargin Ali Baba da Dansa sun zaftarewa alarammomi kudin addu’a da gwamna Ganduje ya ba su a ranar arfa, hakan ya sanya suka gayyaci bangarorin da abun ya shafi domin binciken hakikanin abun da ya faru.

A wata hira da Freedom Radio Ali Baba ya ce sun zaftare kudin da aka bai wa malaman ne domin a samu damar fadada rabon ga sauran malamai wadanda suka yi addu’a daga gida.

Hakama gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan al’amuran addinai na Kano Tahar Adamu Baba Impossible ta ce ba da saninta aka yankarwa malamai kudin addu’ar ba.

Wakilin Freedom Radio Yusuf Ali Abdallah da ya halarci hukumar ta Anti Corruption ya rawaito mana cewa, Ali Baba ya samu rakiyar iyalansa da kuma tawagar mukarrabansa.

Sai dai bayan da ya gama ganawa da shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, ya umarci a zarce da Ali Baba sashen bincike na musamman inda yake amsa tambayoyi a wurin yanzu haka, daga bisani kuma Muhyi Magaji ya ce, ya tafi amsa wata gayyata da hukumar EFCC ta yi masa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!