Labarai
Kai Tsaye : Ganduje na gabatar da kudirin kasafin kudin 2021
A ya yin da kuma ya ambato bangaren ayyuka noma Gwamnan Ganduje ya ce gwamnatin sa ta baiwa wannan bangren fifiko wajen ciyar da kasar nan gaba.
Ganduje ya kuma bayyana cewar, kudirin kasafin kudin badin ya tanadi yadda za’a gudanar da ayyuka a yankuna nan karkara.
Da yake jawabi gwamnan Kano kan yadda za’a kashewa bangaren kiwon lafiya kudi, Ganduje ya ambato cewa ,Gwamnatin sa ta kammala wasu asibitoci da gwamnatocin baya suka faro amma ba su kammala ba.
Daga cikin asibitocin akwai na Giginyu da kuma na kan titin Gidan Zoo.
A halin yanzu gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje na ga batar da kudirin kasafin kudin badi a kwaryar majalisar dokoki ta Kano.
Daga ciki abubuwan da kudirin kasafin kudin ya kunsa akwai shirin tsanya na Almajirai.
You must be logged in to post a comment Login