Labarai
Kai Tsaye : Ganduje zai kashe fiye da Naira biliyan 147 a kasafin kudin badi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa zata kashe fiye da Naira 147,935,302,948 a kudirn kasafin kudin badi, wanda aka yi wa take da” farfado da tattalin arziki da kuma dorewar cigaban rayuwar al’umma”
Ganduje na gabatar da kudirin kasafin kudin badin ne a kwaryar majalisar dokoki ta Kano.
Ganduje ya ce kasafin kudin badin zai maida hankali wajen baza komar tattalin arziki wajen samar da kudaden shiga da zumar kafa harsashin cimma manufofin gwamnati mai ci.
Da yake jawabi shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Abdulaziz Garba Gafasa ya ce majalisar zata fara yin nazari kan kudirin kasafin kudin badin wajen yin Taza da Tsifa.
Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce nan bada jimawa ba majalisar zata kira shugabanin ma’aikatu da hukumomi da sashi-sashi wajen kare kasafin a gaban kwamitocin majalisar.
You must be logged in to post a comment Login