Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

Published

on

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

Har izuwa yanzu jami’an tsaro daban-daban da ma’aikatan gidan adana namun daji dake nan Kano, suna cigaba da kokarin ganin sun cafke Zakin da ya kwace a daren jiya.

Shugaban hukumar gidan adana namun daji na Kano, Sa’idu Gwadabe Gwarzo ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa izuwa yanzu sun samu nasarar gano inda Zakin yake, har ma sun yi masa allura da zata sanya shi bacci, amma har izuwa yanzu bai kai ga galabaita ba, ballantana su samu su cafke shi.

Shima a nasa bangaren kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar mana da cewa har izuwa yanzu suna ta iya bakin kokarin su domin ganin an cafke zakin.

Tun a daren jiya ne dai Zakin ya kubuce daga inda ake tsare da shi, amma bai fita daga harabar gidan Zoo din ba, mahukunta a jihar Kano dai sun bukaci al’ummar dake makotaka da gidan Zoo da su rufe kofofin su a daren.

Ku cigaba da bibiya ana sabunta labarin.

RUBUTU MASU ALAKA:

Kano:Hukumomin gidan Zoo ta musanta cewar gwaggon biri ne ya cinye miliyoyin kudi

Hukumomin gidan Zoo sun ce ‘yan fashi da makami ne suka sace fiye da miliyan 6

hukumar rabon arziki ta kasa za ta fara bincikar bankuna game da haraji

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!