Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje ya bada umarnin a harbe Zakin gidan Zoo

Published

on

Ganduje ya bada umarnin a harbe Zakin gidan Zoo

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin a harbe Zakin nan da ya kubuce daga gidan adana namun daji na nan Kano matukar zai jawo asarar rayuka.

Kakakin hukumar ta adana namun daji Hayatullahi Garba shine ya bayyanawa Freedom Radio haka a zantawar da tayi dashi da yammacin yau ya kuma kara da cewa matukar aka kama wannan Zakin to kasuwa ta bude, domin kuwa zasu yi ciniki ba karami ba daga ‘yan kallo.

Sannan ya bayyana cewa farashin wannan zakin ya kai fiye da miliyan hudu.

Izuwa yanzu dai a iya cewa saura kiris a dakume wannan zakin domin kuwa, tuni kwararrun jami’an da zasu yi masa kwab daya na dab da isowa Kano, kamar yadda ya shaida mana.

Shima kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni suka dana kunamar bindigar su domin yin abinda yakamata matukar Zakin yaki bayar da hadin kai bori ya hau.

RUBUTU MASU ALAKA:

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

An kama motar mai ta bogi a Kano

‘Yan mari sun shaki iskar ‘yanci a Kano

Siyasa: Muntari bai can-canci zama kwamishina ba –Hamza Darma

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!