Labarai
KALANKUWA: Sarakuna da masu ruwa da tsaki sun halarci bikin tunawa da Al’adu da Tarihi a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci taron farfaɗo da tarihi da al’adun Hausawa da ake gudanarwa a Kano, wanda ya samu halartar manyan sarakunan jihar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar al’adu da tarihi.
Taron, wanda aka shirya domin tunawa da tsoffin dabi’u da al’adun gargajiya na Hausawa, yana gudana ne a cikin yanayi na girmamawa da ɗimbin jama’a, tare da nune-nunen kayan tarihi, tufafi, da wasannin gargajiya da suka bayyana asalin al’ummar Kano.
Taron bikin KALANKUWAR yana gudana ne a filin bajakoli dake Kano

You must be logged in to post a comment Login