Manyan Labarai
Kalubalen da muke fuskanta yawan dalibai don basu gurban karatu – Bello Dalhatu
Hukumar gudanarwa ta kwalejin kimiyyar da fasaha ta Jihar Kano, ta ce babban kalubalen da kwalejin ke fuskanta shi ne yawan daliban da ta ke samu
Shugaban kwalejin kwamrade Bello Dalhatu ne ya bayyana hakan a yau ta cikin ’’shirin Barka da Hantsi’’ na nan tashar Freedom Radio, wanda ya maida hankali wajen inganta gurbin karatu a kwalejin.
A cewar sa, yanzu sun fito da sabon tsari bai wa dalibai gurbin karatu da nufin kawo karshen kalubalen da suke fuskanta na yawan dalibai.
Yana mai cewa, kwalejin ta kuma bullo da sabbabin manufofi domin ganin antantance daliban da suka cancanta a basu gurbin karatu.
Ya kuma yi kira ga daliban da suka samu kansu a kwaleji da su mai da hankali akan karantun su.
You must be logged in to post a comment Login