Labarai
Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami
Babban limamin massalacin juma’a na tokarawa Malam Ado Ya’u ya ce shuwagabanin kananan hukumomi su mai da hankali a kan al’ummar da suke jagoranta a nan jihar kano.
Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da taron wayar da kan matasan garin na Tokarawa dake karamar hukumar Nassarawa.
Malam Ado Ya’u ya kara da cewa matasan garin Tokarawa suna fama matsalar makarantar firamare da sakandare da kuma matsalar wutar lantarki.
Matasan garin suna kira da shugaban karamar hukumar nassarawa ya tallafamusu da kayayyakin more rayuwa kasancewar ta hakan ne za su sami cigaba.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa malamai da dattawa da matasa suna kira da Gwamnatin jihar kano data kawo musu dauki a garin nasu ta tokarawa.