Kasuwanci
Kamfanin Mai na Dangote ya gargaɗi ƙungiyar PENGASSAN

Kamfanin Man Fetur na Dangote ya gargadi ƙungiyar ma’aikatan kamfanonin mai da iskar gas PENGASSAN cewa umarnin dakatar da kai mai da iskar gas sassan kasar nan zai iya jefa kasar nan cikin sabon ƙarancin man fetur da tashin farashin sa da asarar kuɗaɗen shiga na gwamnati.
A sanarwar da ya fitar, kamfanin na Dangote, ya bayyana matakin a matsayin hanyar lalata tattalin arziki, ya na mai cewa zai katse samar da kayayyakin da ake buƙata a kullum – kamar su fetur, dizal, man jiragen sama da hakan zai jefa al’umma cikin tsananin wahala.
Matatar ta Dangote ta ce wannan barazana ba kawai zai jefa ‘yan ƙasa cikin matsala ba ne, har ma zai rage kudaden shiga na gwamnati da kuma rage kwarin gwiwar masu saka jari a kasar nan.
Kamfanin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su gaggauta shawo kan lamarin tare da roƙon PENGASSAN ta bi hanyar doka da sulhu, maimakon matakan da za su haifar da rudani da wahala ga Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login