Connect with us

Labarai

Kamfanin NNPC ya ce adadin mai da suke samarwa ya karu

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC, ya ce, adadin danyen man da kasar nan ke fitarwa a duk rana a cikin shekarar da ta wuce, ya karu zuwa ganga miliyan biyu da dubu casa’in wanda ya nuna karin kaso tara cikin dari.

A cewar kamfanin na NNPC a shekarar dubu biyu da goma sha bakwai adadin man da kasar nan ke fitarwa, bai wuce ganga miliyan daya da dubu tamanin da shida ba.

Shugaban kamfanin na NNPC Dr. Maikanti Baru ne ya bayyana haka yayin wani taro don nazartar ayyukan kamfanin a shekarar da ta wuce wanda ya gudana a Abuja.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kamfanin Mr Ndu Ughamadu, ta ruwaito Maikanti Baru na cewa, an samu ci gaban ne sakamakon namijin kokarin da kamfanin bunkasa harkokin man fetur na kasa wato Nigeria Petroleum Development Company (NPDC) ya yi.

Maikanti Baru ya kuma nuna damuwar sa kan halin da matatun man kasar nan su ke ciki, yana mai cewa rabuwar da ayi musu  cikakken gyara tun a shekaru arba’in da biyu da suka wuce.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,745 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!