Labaran Kano
Kamfanonin magunguna na sayar wa asibtocin gwamnati magunguna da tsada
Shugaban rikon kwarya na asibitn koyarwa na malam Aminu Kano Farfesa Abdulrahman Sheshe ya ce ana sayarwa asibitocin gwamnati magunguna a farashi mai tsada yayin da ake sayar wa asibitocin masu zaman kansu a farashi mai rahusa daga bangaren kamfanonin da ke sarrafa wadannan magunguna.
Farfesa Sheshe ya bayyana haka ne a jiya a yayin wata tattaunawa ta fahimtar juna tsakanin wasu wakilan sashin kasuwanci na kamfanin Kula da Magunguna ta duniya.
Shugaban rikon kwaryar ya bayyana yadda ake sayar da magungunan a matsayin abinda ba daidai ba, kuma ya saba da doka da oda, wanda hakan zai iya haifar da rashin jituwa tare da sabawa tsarin amfani da magungunan da ake sayarwa marasa lafiya.
Ya bukaci kamfanonin da ke sarrafa magunguna da su rage farashin magungunan da suke sayarwa ga asibitocin gwamnati a fadin Najeriya.
Farfesa Sheshe ya shawarci wadannan asibitoci da kungiyoyin da ke samar da magunguna ga sibitoci da su yi duba tare da basu ta su gudunmuwar ga alummarsu, a cewarsa gwamnati ita kadai ba za ta iya dukkanin aikin kyatatawa al’ummarta ba, suma al’ummar suna da tasu gudunmuwar da zasu bayar.
Ya ce mafi yawan marasa lafiyar da ke sayan wadannan magungunan marasa galihu ne, da suke bukatar sauki a yayin neman lafiyarsu.
Da yake Magana Toyin Mylan wanda shine ya wakilcin wadannan kamfaoni ya sha alwashin ganin hakan ya tabbata wajen samar da magunguna cikin sauki ga asibitocin kasar nan.