Kasuwanci
Kana boye kayan masarufi mu kuma zamu fasa shagon mu rabawa jama’a – Muhyi Magaji
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta alakanta hauhwar farashin kayayyakin masarufi da cutar corona.
Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimingado ne ya bayyana haka ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom rediyo da safiyar yau.
A cewar Muhyi Magaji tun bayan bullar cutar corona kamfanoni ba sa iya sarrafa kayayyaki kamar yadda ya kamata.
Ya ce, sun tattauna da kamfanoni da dama musamman masu sarrafa sukari, wadanda suka tabbatar da cewa daga farkon azumi zuwa karshensa akwai wadatattceen sukari da zai wadatar da al’ummar Jihar Kano.
Ya kuma jaddada cewa hukumar ba za ta bar ‘yan kasuwa su yi abin da suka ga dama ba a lokacin azumi.
‘‘Domin duk wanda muka kama ya boye kayayyakin masarufi zamu fasa shagon mu rabawa jama’a’’ a cewar Muhyi Magaji Rimingado.
You must be logged in to post a comment Login